Babban Hafsan sojin sama AVM Hassan Abubakar, ya ziyarci mutanen da harin sojojin sama ya samu bisa kuskure a jihar Zamfara.
Mutanen daya ziyarta sun hadar da iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata.
Idan za’a iya tunawa a ranar 10 ga watan Junairun shekarar 2025 ne wani jirgin sojin sama yayi kuskuren kisan fararen hula a kauyen Tungar Kara dake karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, kuma hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan Bijilanti 11.
Cikin wata sanarwa da mataimakan daraktan yada labaran rundunar sojin sama Kabiru Ali, ya fitar a jiya alhamis, rundunar ta bayyana lamarin a matsayin abun da bata ji dadin faruwar sa ba.
Hassan, ya tabbatar da cewa sojin sama ne suka yi kuskuren kisan wanda yan Bijilanti 11 suka mutu tare da jikkata karin wasu mutane 11, yana mai cewa zasu yi kokarin kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Babban hafsan yace rundunar sojin sama zata bawa iyalan wadanda suka rasu sakamakon harin tallafin kudade da kuma sake gina gidajen da harin ya lalata.
A nasa jawabin gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, wanda ya tarbi tawagar AVM Hassan Abubakar, ya bayyana farin cikin sa da rundunar Sojin saman ta kula da lamarin mutanen da aka kaiwa harin.