Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023 Alhaji Murtala Sule Garo ya mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya daban-daban su ka fara gudanar da ibadar azumin watan Ramadan.
Yace tabbas wannan babbar dama ce a garemu ta inganta alakarmu da Ubangiji maɗaukakin sarki ta hanyar habaka ibadarmu da neman yafiyarsa.
Murtala Sule Garo, yayi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar musulmi dan yin koyi da dabi’un Annabin rahama amincin Allah ya tabbata a gareshi wajen nuna tausayi da jinkai da karamci da kuma taimakawa marasa karfi.
Yace wannan wata mai alfarma dama ce ta tunawa da marasa karfi a cikin mu tun daga ‘yan uwa da makwafta har izuwa sauran al’umma.
Hakazalika yayi kira ga al’ummar jihar Kano da su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da cigaba da yalwar arziki.
Daga karshe Alhaji Murtala yayi addu’ar Allah ya karbi ibadun mu ya kuma sa mu kasance cikin bayin da zai yanta.