Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha tsawon watanni 6.
Majalisar ta yanke hukuncin dakatarwar yayin zaman ta na yau Alhamis wanda Shugaban majalisar Godswill Akpabio, ya jagoranta.
Tunda farko kwamitin ÆŠa’a na majalisar ne ya bayar da shawarar daukar matakin dakatarwar, bayan da Natasha ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita.
Bayan dakatarwar majalisar ta dakatar da albashin Natasha na tsawon lokacin da aka haramta mata zuwa majalisar, sannan za’a janye mata jami’an tsaron dake tsaron lafiyar ta.