Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ƙarfin wutar lantarkin da ake samarwa a Najeriya yakai wani mataki da ba’a taba samun irin sa ba.
Gwamnatin tace a yanzu haka an samu karuwar lantarkin zuwa megawatts 6,003.
Wata sanarwa da Bolaji Tunji, mai ba da shawara na musamman kan dabarun sadarwa ga ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya fitar tace ba a taɓa samun ƙarfin wutar lantarki kamar wannan ba a tarihin Najeriya.
Sanarwar tace hakan ya biyo bayan samun ƙarfin wutar lantarki mafi girma da aka samu na megawatts 5,801.84.
Ya ce nasarorin da aka samu suna nuna gagarumin ci gaba a fannin samar da wutar lantarki da ake samu a kasar nan, da gyare-gyaren da ake yi a bangaren samar da wutar lantarki.