Matar aure ta kashe kishiyar ta, ta ƙone gawar ta

0
93

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka samu gawarta a gidan Mijin ta a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.

Rahoton da aka kai wa ‘yan sanda a ranar 3 ga Maris, 2025, ya nuna cewa an samu shakku kan yadda Hajara ta rasu, inda iyalanta suka zargi kishiyarta da hannu a lamarin.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad, ya ba da umarni na gaggawa ga tawagar bincike daga C Divisional Police Headquarters, karkashin jagorancin DPO, domin gudanar da bincike mai zurfi.

Binciken farko ya kai ga kama wata mata mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28, wadda ita ce kishiyar mamaciyar. Da aka bincike ta, ta amsa cewa ita ce ta shake Hajara ta mutu sannan ta yi kokarin boye laifin ta hanyar zuba mata ruwan zafi da kona gawarta da buhun robobi.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa za’a ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), domin tabbatar da an gurfanar da masu hannu a kisan a gaban shari’a. Binciken zai hada da amfani da fasahohin zamani da kuma tono gawar mamaciyar idan bukatar hakan ta taso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here