Gwamnatin Yobe ta dena biyan albashi ga ma’aikatan ta su 5,029, sakamakon rashin bayyanar su a gaban kwamitin tantance ma’aikatan jihar daya gudana.
An cire mutanen daga tsarin albashin jihar Yobe mai ma’aikata 32,140, kamar yadda shugaban kwamitin tantance ma’aikatan Bukar Kilo, ya sanar a ranar Talata, lokacin da yake gabatar da rahoton daya tattara ga shugaban ma’aikatan jihar a birnin Damaturu.
Bukar Kilo, shine kuma babban sakataren ofishin shugaban ma’aikatan jihar ta Yobe, inda yace kwamitin sa ya samu damar tantance ma’aikata 27,111, a aikin tantance ma’aikatan daya gudana tsakanin watan Yuni na shekarar 2024 zuwa Fabrairu na shekarar 2025.
A nan ne yace 5,029, daga cikin adadin ma’aikatan da aka ce jihar tana dasu basu bayyana a yayin tantancewar ba, yana mai cewa hakan ya saka shakku akan cewa adadin mutanen ba cikakkun ma’aikata bane.
A nasa jawabin shugaban ma’aikatan jihar Yobe Tonga Betara, ya bayyana yabon sa ga kwamitin tantance ma’aikatan akan sadaukarwar da suka yi, har aka samu nasarar kammala tantancewar.