Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da kudirin bukatar kafa rundunar Hisbah bayan yin zama na uku akan kudirin a ranar Talata.
Kakakin majalisar dokokin Jigawa Haruna Aliyu Dangyatin, tare da mambobin majalisar dokokin jihar ne suka kammala zama da kuma tantance bukatar kafa hukumar Hisbar.
Gwamnan Jigawa Umar Namadi, ne ya aikewa majalisar dokokin kudirin wanda kuma majalisar ta amince dashi.
Rundunar Hisbah dai na taimakawa jihohin musulmi a Najeriya wajen dakile yaduwar mummunar dabi’a musamman rashin tarbiyya a tsakanin matasa.