Tafiye-tafiyen Tinubu sun samarwa Najeriya Dala Biliya 50—Gwamnatin tarayya

0
70

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa tafiye-tafiyen da shugaban kasa Bola Tinubu, ya rika yi zuwa kasashen ketare sun janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, da hakan yasa aka samu shirin zuba jarin dala biliyan 50.8 a kasar nan.

:::Gwamnonin Jigawa, Kebbi da Bauchi sun rage lokacin tashi daga aiki

Ministar Kasuwanci masana’antu da zuba jari ta kasa Jumoke Oduwole, ce ta sanar da hakan a yau Talata lokacin da take ganawa da manema labarai a Abuja.

Ministar tace tattalin arzikin Najeriya yana bukatar zuba masa jarin da yakai dala biliyan 50, don samun ingantuwa musamman a fannin musayar kudaden ketare, tana mai cewa akwai bukatar shirin zuba jarin ya kawo sauyin da ake nema a kasar nan.

Ta kara da cewa zuwa watan Disamba na shekarar 2024, tafiye-tafiyen da Tinubu yayi sau 30, ya sanya Najeriya samun zuba jarin dala biliyan 50.8.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here