Kamfanin tattara lantarki na kasa TCN, yace a yanzu haka Najeriya ta tattara lantarkin da karfin ta yakai Megawatts 5,713.60, yana mai cewa ba’a taba samun irin wannan wuta ba a shekaru 4 da suka gabata.
:::Dan shekara 20 ya kashe mahafiyar sa da Tabarya
TCN, ya sanar da hakan cikin wata sanarwar da aka fitar a yau Talata, tare da cewa wannan adadi shine mafi girma da aka samu a wannan shekara ta 2025, kuma an rarraba lantarkin zuwa manyan turakun lantarkin dake fadin kasar nan.
Kamfanin ya kara da cewa an samu karuwar wutar akan wadda aka samu a ranar 14, ga watan Fabrairu wanda aka samu wutar da karfin ta yakai megawatts 5,543.30.