Ma’aikata sun nemi a kori shugabn jami’a bisa zargin lalata da ma’aikaciya

0
56

Kwamitin mata na Kungiyar manyan ma’aikatan jami’i’o’i wadanda ba malamai ba SSANU sun nemi a cire shugaban Jami’ar tarayya ta Ekiti, Farfesa Abayomi Fasina, daga mukaminsa bisa zargin sa da neman lalata da daya daga cikin wata mace mamba a kungiyar.

Mambobin SSANU, mata sun nemi uwar gidan shugaban kasa Remi Tinubu, matan gwamnoni, majalisun dokokin kasa, ministan ilimi, da matan kungiyar kwadago su shiga cikin wannan lamari, ko kuma su gudanar da zanga-zanga a majalisun dokokin kasa in har aka gaza daukar mataki akan Abayomi.

:::Dan shekara 20 ya kashe mahafiyar sa da Tabarya

Sai dai shugaban Jami’ar yace bashi da wata masaniya akan zargin neman yin lalata da ma’ailaciyar, yana mai cewa yan sanda sun gudanar da bincike akan zargin kuma sun wanke shi a rahoton da suka tattara.

Abayomi, ya kuma bayyana zargin a matsayin kokarin bata masa suna.

A halin da ake ciki an kafa wani kwamitin cikin gida a jami’ar ta Ekiti mai mutane 9 wanda aka bashi aikin gudanar da binciken zargin da kuma bayyana abin daya gani, duk da cewa Fasina yayi jawabin cewa matar da ake zargin yana neman yin lalata da ita bata yi wani kalami dake nuna cewa yayi kokarin cin zarafin ta ba a lokacin da take jawabi ga kwamitin da aka samar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here