Wata Kotun majistri dake Kano ta yankewa yan TikTok biyu hukuncin zaman gidan yari na shekara daya kowannen su.
:::Obasa ya sake zama kakakin majalisar dokokin Lagos
Kotun ta samu Æ´an TikTok É—in da laifin wallafa bidiyo na rashin tarbiyya sannan suka ci karo da addinin muslinci.
Wadanda aka yankewa hukuncin sune Ahmad Isa da Maryam Musa, yan unguwar Ladanai dake Hotoro.
An yiwa yan TikTok din shari’a a Kotun Majistiri da ke zamanta a gini mai lamba 47 a unguwar Norman’s land, da ke Æ™aramar hukumar Fagge, karkashin jagorancin mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan.
Tunda farko hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ce ta kama matasan biyu, gabanin gurfanar dasu.
Mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan, tace yan TikTok din suna da zabin biyan tarar Naira dubu 100 kowannen su, in har basa bukatar zaman gidan yari.