Gwamnonin Jigawa, Kebbi da Bauchi sun rage lokacin tashi daga aiki

0
40

Gwamnonin Jigawa da Bauchi Bala Muhammad da Umar Namadi, da gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris sun rage lokacin tashi daga aikin ma’aikata saboda Azumin Ramadan.

Ma’aikatan zasu rika yin aiki daga karfe 9 na safe zuwa 3 na yammacin ranakun Litinin zuwa Alhamis, yayin da a ranar juma’a zasu tashi daga aiki da karfe 1 na rana, a jihar Jigawa

Ita kuwa jihar Kebbi tace ma’aikatan jihar zasu rika yin aiki daga karfe 8 zuwa 1 na rana a ranakun Litinin zuwa Alhamis, sai karfe 8 zuwa 12 a ranar Juma’a.

Hakan yazo a daidai lokacin da Kungiyar Kristocin Najeriya ta bayyana kalubalantar gwamnonin Kano, Bauchi Jigawa, Kebbi da Katsina akan rufe Makarantun Boko don shigowar azumi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here