A karon farko farashin gangar danyen man fetur ya karye a kasuwannin duniya zuwa dala 70, tun bayan watan Oktoban shekarar 2024.
Farashin ya sauka da kaso 1.2, zuwa dala 70.76, yayin da danyen man Amurka na WTI, ya samu saukar farashi da dala 0.86, zuwa dala 67.77, a yau da misalin karfe 06:04, agogon Amurka.
:::Tafiye-tafiyen Tinubu sun samarwa Najeriya Dala Biliya 50—Gwamnatin tarayya
Karyewar farashin yazo a daidai lokacin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC, tace zata kara yawan man da take samarwa kasuwa a watan Afrilu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito cewa dama shugaban Amurka Donald Trump, ya matsa kaimi ga kasar Saudiyya da OPEC, akan su yi kokarin rage farashin danyen man.