Ƴan ta’adda sun sace jagororin jam’iyyar APC su biyar

0
56

Wasu yan ta’adda sun sace jagororin jam’iyyar APC su biyar a jihar Zamfara dake arewacin Nijeriya.

Mai sharhi akan al’amuran tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama, ya wallafa a shafin sa cewa magoya bayan APC da aka sace yan asalin karamar hukumar Kaura Namoda, ne da suke kan hanyar sure ta zuwa Marafa don ziyartar gidan Sanata Abdulaziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Daga cikin su akwai Yahaya Sani Dogon Kade, shugaban mazabar Dan Isah, da kuma Bello Dealer, shugaban mazabar Sakajiki.

Zuwa lokacin rubuta wannan labari ba’a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Zamfara ba akan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here