Zan goyi bayan samar da sabuwar jiha daga Katsina—Sanata Barau

0
63
Jibrin-Barau

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Barau I Jibrin ya ce zai yi aiki tare da Sanata Muntari Dan-Dutse mai wakiltar yankin Funtua ta jihar Katsina domin tabbatar da ƙirƙiro jihar Karaɗuwa daga jihar dake yankin arewa maso yamma.

Barau yace samar da sabuwar jihar zai inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar  Karaɗuwa.

Sanatan yace Karaɗuwa nada duk wasu abubuwan da ake so don zama jiha mai cin gashin kanta, sai dai Barau yace kirkiro jiha abu ne mai wahalar gaske, amma du da haka zai goyi bayan bukatar al’ummar yankin ta neman jiha.

Barau ya bayyana haka ne a lokacin da yake jagorantar rabon tallafin kayan abinci na azumi ga dubban ƴan yankin wanda Sanata Muntari ya ɗauki nauyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here