Za’a gudanar da sabon zaɓen kananun hukumomi a Rivers

0
24

Gwamnan jihar Rivers Siminalaya Fubara, ya umarci shugabannin kananun hukumomin jihar su sauka daga mukamin su.

Yace za’a gudanar da sabon zaɓen kananun hukumomi a nan gaba.

Hakan ya biyo bayan yanke hukuncin da kotun koli tayi a ranar juma’ar data gabata, wanda ta soke zaben kananun hukumomin Rivers bisa hujjar cewa hukumar zaben jihar tayi abubuwan da suka saba ka’ida a lokacin da aka gudanar zaɓen kananun hukumomin.

Fubara yace daraktocin gudanarwar kananun hukumomin jihar ne zasu cigaba da rike mulkin kananun hukumomin zuwa lokacin da za’a zabi sabbin shugabanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here