Muna kira da a tsagaita wutar cin mutuncin juna—Abdullahi Abbas

0
147

Shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas, yayi alkawarin ajiye siyasar hamayya da cin zarafi saboda watan Azumin Ramadan.

Shugaban jam’iyyar ya nemi duk wasu yan siyasa dasu tsagaita wuta irin ta siyasar hamayya da cin zarafin juna.

Yace yanzu lokacin sada zumunci ne da kaunar juna da kuma taimakawa al’umma.

Abdullahi Abbas, ya kuma nemi a fito da tallafin kayan abinci domin rabawa mabukata a wannan lokaci mai albarka.

Kafin yanzu dai an samu bayyana kalaman tunzuri tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa a Kano musamman bangaren APC da NNPP kwankwasiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here