Matatar Dangote zata mayarwa yan kasuwar da suka siya fetur a farashin daya zarce Naira 825, kan kowacce Lita kudaden su don saukakawa yan Najeriya.
Mayar da kudaden zai saka matatar yin asarar Naira biliyan 16.
Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur daga Naira 890 zuwa Naira 825 saboda a saukakawa yan Nijeriya a lokacin Azumin Ramadan, wanda matatar tayi makamancin wannan ragi a yayin bukuyum kirsimeti da sabuwar shekarar 2025.
Matatar ta kuma yi ala wadai da yan kasuwar da take siyarwa da mai a farashi da sauki su kuma su tsauwalawa mutane farashin.
Matatar tace babu tausayi ga yan kasuwar da suke siyan man akan farashin naira 825, sannan su siyar a farashin Naira 945 ko sama da haka.
Matatar Dangote dai ta sanar da rage farashin litar man ta daga Naira 890 zuwa Naira 825, don alfarmar watan Ramadan.