Hisba ta kama matasan da ba sa yin azumi a Kano

0
48

Jami’an rundunar Hisba ta jihar Kano sun kama wasu matasa da ake zargi da kin yin azumin farko na watan Ramadan da aka fara a jiya Asabar.

Mataimakin babban kwamandan rundunar, Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar ne ya sanar da hakan ga manema labarai.

Yace an kama matasan yayin gudanar da sintiri da jami’an hukumar ke yi a sassa daban-daban na Kano.

Hisbah ta Kuma kama wasu mutane 60 da suka yi askin banza a kansu.

Har ila yau Hisba ta kama wasu direbobin babura masu kafa uku akan zargin su da haɗa maza da mata a baburansu.

Hisba ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri don tabbatar da bin ka’idar da shari’ar muslinci ta gindaya  a wannan wata na Ramadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here