Cocin Evangelical ta rabawa Musulmai 1000 kayan abincin Ramadan

0
31
Kaduna

Cocin Evangelical ta rabawa al’ummar Musulmin jihar Kaduna kayan abinci saboda Azumin Ramadan.

Akalla Musulmai 1000, aka bawa kayan abincin a yankin Sabon Tasha dake karamar hukumar Chikun.

Makarantun Islamiyya na daga cikin inda aka raba tallafin.

Malamin cocin Yohanna Buru, yace an raba tallafin don karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmai da Kristocin yankin.

Yace sun kuma kwaikwayi alkairin da wata mata mai suna Hajiya Ramatu Tijjani, keyi inda take bawa Kristoci kayan abinci a lokacin kirsimeti.

Kungiyoyin masu bukata ta musamman suma sun karbi tallafin kayan abincin na Cocin Evangelical.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here