Malaman Firamaren Kano sun bayyana adadin kudin da aka zaftare a albashin su

0
42

Da yawa daga cikin malaman makarantun Firamare dake jihar Kano sun shiga kunci da damuwa dangane da abinda suka ce an zaftare musu albashin watan Fabrairu daya gabata ba tare da sanin dalili  ba.

Jaridar Kano Times, tace wasu daga cikin malaman an yanke musu Naira dubu 18 daga albashin yayin da aka cirewa wasu Naira dubu 33.

Wadanda abin ya shafa sun ce ba’a sanar da su dalilin yin hakan ba, duk da cewa sun yi aiki tukuru kafin lokacin karbar albashin nasu da suka ga abinda basu yi zato ba.

Shima daya daga cikin shugabannin Kungiyar malaman Firamaren mai suna Malam Usman Abdullahi, yace an yanke masa naira dubu 33, a albashin nasa, sannan yace hakan abin yin ala wadai ne saboda ana fama da tsadar rayuwa.

Tuni dai gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya sanar da daukar matakin kafa kwamitin da zai binciki dalilin daukar wani abu daga albashin ma’aikata, tare da korar mai rikon shugaban ma’aikatan jihar bisa zargin sa da hannu a lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here