Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasa EFCC, Ola Olukoyede, yace Najeriya na yin asarar sama da Naira biliyan 40 duk shekara sakamakon damfarar da ake yi wajen daukar ma’aikata.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata ganawa da jami’an Kungiyar Tattaunawa da Ma’aikata ta kasa (NECA) a babban ofishin EFCC na Abuja.
Ya ce binciken da ya gudanar a shekarar 2007 kafin ya shiga hukumar EFCC ya gano cewa ma’aikata suna cutar juna ta hanyoyi daban-daban.
Ola Olukoyede, ya ce tun bayan hawan sa shugabancin EFCC, hukumar ta bankado miliyoyin kudi bayan ta gano cewa akwai marasa aiki da ke karbar albashi daga gwamnatin tarayya.