Gwamnatin kasar Amurka ta dauki matakin dakatar da tallafin kudin da take zubawa a asusun kula da kananun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF.
Asusun UNICEF shine ya sanar da daukar matakin na Amurka, wanda a kwanakin baya kasar ta sanar da jingine ayyukan hukumar USAID da take taimakawa a kasashen duniya wajen bayar da tallafin jin kai.
Dena bayar da tallafin da Amurka ta yiwa UNICEF zai sanya dakatar da wasu ayyukan tallafawa kananun yara a sassan duniya da dama.
Asusun ya ce ɓangarorin da matakin ya shafa sun haɗa da na tallafa wa ƴan gudun hijira da yaƙi da cutar shan inna da kuma mai karya garkuwar jiki HIV.
Asusun ya ce matakin na Amurka zai haifar da ƙaruwar mace-macen ƙananan yara.