Sheikh Daurawa ya gana da Ganduje

0
27

Bayan tsawon lokaci a yau shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gaisa da shugaban babban kwamandan rundunar Hisbah ta jihar Kano Malam Aminu Ibrahim Daurawa.

Malamin ya hadu da Ganduje, a wajen bikin daurin auren Gata na Maza 300, Mata 300, wanda gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyi, kuma aka gudanar a ranar Alhamis.

Idan za’a iya tunawa an samu takun saÆ™a tsakanin shugaban na APC da Sheikh Daurawa lokacin da yake shugabantar Hisbah a zamanin mulkin Ganduje, wanda hakan ya zama sanadiyyar barin Daurawa hukumar Hisbah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here