Kotun koli ta hana CBN turawa gwamnatin Rivers kudi 

0
27

Kotun kolin kasar nan ta dakatar da babban bankin kasa CBN da babban akanta janar na kasa da sauran hukumomin kudi turawa gwamnatin Rivers kudi daga asusun gwamnatin tarayya.

Hukuncin kotun yace za’a daina tura kudi ga Rivers har zuwa lokacin da za’a samar da majalisar dokokin jihar mai tafiya akan tsarin doka da ka’ida.

Mai Shari’a Emmanuel Akomaye, ne ya yanke hukuncin a madadin sauran alkalan kotun su 5, kuma aka yi watsi da bukatar gwamnan jihar Siminalaya Fubara, daya daukaka kara.

Fubara, ya daukaka kara akan kalubalantar shugabancin majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, bayan ya gabatar da kasafin kudin jihar ga yan majalisa 4, tare da kin amincewa da masu yin biyayya ga ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike.

Kotun ta kuma umarci Martin Amaewhule, da sauran yan majalisar dokikin Rivers su koma aiki kamar yadda suka saba a baya ba tare da bata lokaci ba.

Alkaline kotun kolin yace bai dace ba ace Fubara ya gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2025 ga mambobin majalisar dokokin jihar su 4 kacal, ba tare da bawa mazabu 28 damar bayyana ra’ayoyin su akan kasafin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here