Kotu koli ta rushe zaben kananun hukumomin jihar Rivers

0
19

Kotun koli ta sanar da rushe zaben kananun hukumomin jihar Rivers daya gudana a ranar 5 ga watan Oktoba na shekarar 2024, inda tace zaben yaci karo da ka’idojin doka.

Alkalai 5 na kotun kolin sun ce hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Rivers ta gaza cika ka’idojin da ake bukata kafin shiryawa da gudanar da zaben.

Mai shari’a Jamilu Tukur, ne ya sanar da yanke hukuncin wanda ya rushe daukacin shugabannin kananun hukumomin jihar da kansilolin da aka a baya.

Idan za’a iya tunawa a safiyar yau juma’a ne dai kotun kolin ta zartar da hukuncin hana babban bankin kasa CBN turawa jihar Rivers kudi daga asusun gwamnatin tarayya, saboda rikicin shugabancin majalisar dokokin jihar wanda kotun ta amince da yan Majalisar Rivers masu goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here