Al’ummar Zamfara sun shiga damuwa akan biyan yan ta’adda kudin fansa

0
17

Jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da fuskantar ayyukan ta’addanci daga masu garkuwa da mutane da shanu da kuma kisan gilla babu gaira babu dalili.

Zuwa yanzu wannan yanayi yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da kuma asarar dukiya tare da rasa muhallin zama ga wasu mutanen.

A yanzu haka mutanen dake yankunan Zurmi da Shinkafi, sun koka akan biyan yan ta’adda kudin fansa da yakai Naira miliyan 300.

Wasu kauyukan kuwa suna cikin fargabar hare hare da satar dabbobi hadi da kayayyakin abinci.

Karuwar ayyukan rashin tsaron ya biyo bayan kwashe jami’an sojin da aka yi daga yankin a Litinin din data wuce.

Dan majalisar dake wakiltar Zurmi da Shinkafi a zauren majalisar wakilai Bello Hassan Shinkafi, shine ya shaidawa BBC cewa al’ummar yankin sa na cikin halin rashin tsaro bayan janye ma’aikatan tsaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here