Tsohon shugaban kasa Buhari ya koma jihar Kaduna

0
83

A karon farko tsohon shugaban kasa Buhari, ya koma gidan sa dake jihar Kaduna, tun bayan saukar sa daga shugabancin Najeriya.

Cikin wadanda suka yiwa tsohon shugaban kasar rakiya zuwa gidan na Kaduna akwai mataimakin shugaban kasa Ƙashim Shettima, Gwmanan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da gwamnan jihar Kaduna Uba Sani.

Suma wasu daga cikin tsaffin ministocin gwmanatin Buhari, sun samu damar yi masa rakiya.

Yau kusan shekara 2, kenan da Buhari ya bar mulkin Najeriya inda ya koma mahaifar sa dake Daura a jihar Katsina.

Buhari, ya bar mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, zuwa hannun shugaban kasa Bola Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here