Sarkin musulmi ya bayar da umarnin fara duban jinjirin watan Ramadan

0
38

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta umarci al’ummar Musulmin Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan daga gobe Juma’a.

Bayanin fara duban jinjirin watan na cikin wata sanarwa da fadar ta aikewa kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Sokoto dauke da kwanan watan yau Alhamis, 27 ga watan Fabrairu tare da sanya hannun Farfesa Sambo Wali Junaidu Wazirin Sokoto, wanda kuma shine shugaban kwamitin bayar da shawara akan harkokin addinin muslinci na masarautar Sokoto.

Sanarwar tace mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, yana umartar mutane su fara duban jinjirin watan Ramadan daga gobe Juma’a, sakamakon juma’ar itace ranar da watan Sha’aban ke cika kwanaki 29.

Idan an samu ganin watan a gobe za’a tashi da azumin Ramadan a ranar asabar, in kuma ba’a samu damar ganin jinjirin watan Ramadan din a juma’a ba sai Lahadi za’a wayi gari da azumin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here