Mayakan Boko Haram sun bankawa gidaje da masallatai wuta a Adamawa

0
50

Yan ta’addan Boko Haram sun kai wani mummunan hari kauyen Kwampre dake sabuwar Yadul ta karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.

Harin da mayakan suka kai a cikin dare yayi sanadiyyar kone gidaje, guraren ibada, shaguna da makarantu.

Lamarin ya faru a ranar Talata data gabata kafin Sallar Isha, kuma sun jima suna yin abunda suka ga dama a kauyen, tare da sace dukiyar al’umma mai yawa bayan kone musu gidaje da wajen sana’ar su ta yau da kullum.

Mai unguwar kauyen Kwampre Joel Kulaha, ya tabbatar da kai harin, amma ya ce ba a samu asarar rai ba, sai dai ta dukiya. Joel, yace da yawa daga cikin mutanen garin sun gudu don tsira da rayuwar su.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin dake yankin Garaha da ke kusa da inda aka kai harin sun kai É—auki ga mutane inda suka yi artabu tare da korar maharan.

Amma mutanen garin sun yi zargin cewar jami’an tsaron sun yi jinkirin zuwa, da hakan ya sa mayakan suka yi ɓarna fiye da tunani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here