Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana takaicinsa kan rahotannin da suka nuna ana rage albashin wasu ma’aikatan gwamnati ko kuma hana su albashinsu gaba ɗaya, yana mai cewa hakan babban cin zarafi ne ga haƙƙin ma’aikata kuma cin amanar jama’a.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
Gwamna Yusuf, wanda ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan labarin cewa wasu ma’aikata sun kwashe watanni ba tare da an biya su haƙƙinsu ba, ya yi alkawarin binciko masu hannu a wannan aika-aika tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansu.
Yace wannan gwamnati ba za ta lamunci zalunci ga ma’aikata ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika, doka za ta yi aiki a kansa ba tare da rangwame ba.
A wani mataki na kawo ƙarshen wannan matsala, gwamnan ya kaddamar da wani kwamitin bincike mai ƙarfi don gano musabbabin matsalar, ko dai matsalar fasaha ce ko kuma ganganci da gangan da wasu suka aikata.
Kwamitin zai gudanar da bincike na musamman kan albashin ma’aikatan gwamnati daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025, domin gano waɗanda abin ya shafa, tantance irin asarar da aka yi, tare da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar da kuma hukunta masu hannu a ciki.
Kwamitin yana da mambobi bakwai, wanda Hon. Abdulkadir Abdussalam, Kwamishinan Harkokin Karkara da Ci gaban Al’umma, kuma tsohon Akanta-Janar na Jihar Kano ke jagoranta, ya ƙunshi ƙwararru a fannin kuɗi da tsarin biyan albashi.
Daukacin yan kwamitin sun hadar da;
1. Hon. Abdulkadir Abdussalam – Shugaban Kwamitin
Kwamishinan Harkokin Karkara da Ci gaban Al’umma
2. Dr. Bashir Abdu Muzakkari – Memba
Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Tattalin Arzikin Zamani (Digital Economy)
3. Dr. Aliyu Isa Aliyu – Memba
Daraktan Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano
4. Dr. Hamisu Sadi Ali – Memba
Daraktan Hukumar Sarrafa Basussuka ta Jihar Kano
5. Hajiya Zainab Abdulkadir – Memba
Daraktar Cibiyar Kwamfuta ta Jihar Kano
6. Aliyu Muhammad Sani – Sakataren Kwamitin
Daraktan Bincike da Tantancewa, Ofishin Sakataren Gwamnati
7. Ummulkulthum Ladan Kailani – Mataimakiyar Sakataren Kwamitin
Babbar Mataimakiyar Sakataren Gudanarwa, Ofishin Sakataren Gwamnati
An ba wa kwamitin wa’adin kwana bakwai domin ya kammala binciken sa tare da gabatar da cikakken rahoto kan masu hannu a lamarin, girman barnar da aka yi, da kuma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.