Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a Kofar Nassarawa

0
332

Jami’an yan sanda sun tarwatsa wasu matasa masu shirin gudanar da zanga zanga a Kofar Nassarawa dake birnin Kano.

Masu zanga zangar sun taru a karkashin gadar sama dake Kofar Nassarawa, wanda suka halarci wajen a cikin motoci, duk da cewa kawo wannan lokaci ba’a bayyana dalilin shirya gudanar da zanga zangar ba, amma jami’an yan sanda dana DSS sun tarwatsa aniyar taruwar.

Jami’an tsaron fadar gwamnatin Kano sun yi shirin ko ta kwana don tunkarar duk wani abu da kaje yazo, sakamakon cewa wajen da matasan suka taru hanya ce da zata kai mutun gidan gwmanatin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here