Shugabancin NNPP na kasa yayi watsi da dakatarwar su Kawu Sumaila

0
27

Shugabancin jam’iyyar NNPP a matakin kasa yayi watsi da dakatarwar da aka yiwa su Kawu Sumaila daga jihar Kano.

NNPP ta bakin sakataren ta na kasa Oginni Olaposi, ta fitar da sanarwar cewa dakatarwar ba komai bace face yaudarar kai da shugaban NNPP bangaren Kwankwaso ya yiwa kansa.

A ranar litinin data gabata ne shugaban NNPP bangaren na Kano Hashimu Dungurawa, ya sanar da cewa sun dakatar da Sanata Kawu Sumaila, da Ali Madaki, da Kabiru Alhassan Rurum, da Abdullahi Sani Rogo, bisa zargin su da cin amanar jam’iyyar.

Oginni Olaposi, yace NNPP, tsagin Kwankwaso basu da hurumin dakatar da kowanne dan jam’iyya.

Sakataren ya kara da cewa duk wadanda aka dakatar har yanzu cikakkun yan jam’iyyar NNPP ne daidai da kowa na jam’iyyar.

Oginni Olaposi, yace tun tuni sun kori madugun kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, daga NNPP Dan haka bashi da yancin yin magana a matsayin dan jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here