Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana shirin sa na siyarwa attajirai daga sassan duniya shaidar izinin zama a kasar sa akan Dala miliyan 5 ga kowanne mutum daya, inda yace manyan attajirai daga Rasha zasu samu wannan dama.
Trump, yace wannan Sabon tsarin bayar da izinin zama a kasar sa zai kirkiro sabbin damar ayyukan yi da rage yawan bashin da ake bin Amurka.
An yiwa sabuwar shaidar zama a Amurka lakabi da (Gold Card) wato katin Zinare.
Shima sakataren kasuwanci na Amurka Howard Lutnick, ya goyi bayan fara siyar da sabuwar shaidar zama a kasar, wanda yace bashin da ake bin su zai ragu in aka tabbatar da wannan tsari.
Daman wasu kasashe turai sun nuna damuwa akan yadda Trump, ya bayar da damar tattaunawa da kasar Rasha kai tsaye don kawar da yaƙin Ukraine.
Haka zalika ya sanar da manema labarai cewa akwai yiwuwar ya cire takkukuman da Amurka ta kakabawa Rasha idan hali yayi.