Rundunar yan sandan Taraba ta kama yan fashi da makami

0
16

Rundunar yan sandan kasa reshen jihar Taraba ta sanar da samun nasarar kama wasu mutane da ake zargin yan fashi da makami ne su 20.

Cikin wata sanarwar da rundunar ta sanar a shafin ta na X tace an kama mutanen a yau laraba lokacin da aka kai hari maboyar su dake cikin wata gonar shinkafa a Wamunchi.

:::Kuwait zata taimakawa adadi mai yawa na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya

Cikin abubuwan da aka samu a wajen bata garin akwai bingiga kirar AK-47, da harsashi kunshi 7, sai bindigar gargajiya guda 3, da kwari da baka sai babur mai kafa biyu guda 1.

Jihar Taraba dai na fama da matsalolin tsaro daga lokaci zuwa lokaci, wanda a kwanakin baya ma rundunar yan sandan jihar ta sanar da kama wasu da ake zaton yan kungiyar boko haram ne da suka je jihar da manufar kafa sansanin yin garkuwa da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here