Rundunar yan sandan jihar Kano tace ta zube jami’anta a kwaryar birnin Kano sakamakon bayanan sirrin data samu dangane da masu shirin gudanar da wata zan-zangar da ka’iya haifar da tarzoma.
Cikin wata sanrwar da kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya tabbatarwa da al’umma cewa sun samar da isassun jami’an da zasu samar da zaman lafiya da kuma dakile duk wani yunkurin karya doka a Kano.
:::Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha sun shiga yajin aiki a Kano
Sanarwar ta ja kunnen daidaikun mutane da kungiyoyi akan su gujewa duk wani abun da ya shafi yin karan tsaye ga doka.
A safiyar yau Laraba ne aka samu rahotannin cewa wasu matasa sun shirya gudanar da zanga-zanga a Kofar Nassarawa, da hakan yasa jami’an tsaro tarwatsa su, tare da zube ma’aikata a hanyar zuwa gidan sarki na Nassarawa, da kewaye inda sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ke zaune.