Mayakan Boko Haram sun sace kayan abinci da mutane biyu

0
218

Tawagar yan ta’addan boko haram ta kai wani hari karamar hukumar Jere ta jihar Borno wanda hakan ya basu damar sace mutane biyu da kayan abinci na kudade masu yawa.

:::Rundunar yan sandan Taraba ta kama yan fashi da makami

Sun kai harin ne a kauyen Kaleri, dake karamar hukumar ta Jere, kamar yadda wata majiya ta tabbatar da cewa abin ya faru a kusa da jami’ar Maiduguri.

Majiyar tace mayakan dauke da manyan makamai sun rika bi gida bayan gida tare da neman kayan abinci, tare da saka firgici ga mutanen yankin.

  • Wata majiya data nemi a sakaya ta tace yan boko haram din sun sace mutane 2, sannan suka kwashi kayan abinci suka tsere dasu.

Faruwar harin ke da wuya yan sanda suka rufe hanyar inda lamarin ya faru sannan suka kama wasu mutane biyu, duk da dai ba’a ce suna daga cikin mayakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here