Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun shiga yajin aiki.
:::Shugaba Tinubu yace rashin cire tallafin fetur zai iya ruguza Najeriya
Majiyar Hikima Radio ta rawaito cewa Kafin ma’aikatan su tsunduma yajin aikin sai da suka gudanar da sallah tare da alqunut don neman Allah kawo musu dauki sakamakon mawuyacin halin da suka ce suna ciki.
Ma’aikatan sunce shiga yajin aikin yana da nasaba da yadda gwamnatin Kano taki fara biyan su sabon tsarin mafi karancin albashi na naira dubu 71, wanda tuni ake biyan ma’aikata a jihar. Sun kuma ce akwai wasu karin hakkokin su da gwamnatin ta rike musu.
Dukkanin kokarin da aka yi na jin ta bakin shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, akan lamarin abun ya ci tura.