Kuwait zata taimakawa adadi mai yawa na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya

0
14

Mahukuntan kasar Kuwait, sun sanar da shirin taimakawa kananun yara kimanin dubu dari 2, da basa zuwa makaranta a jihar Kaduna.

:::Shugabancin NNPP na kasa yayi watsi da dakatarwar su Kawu Sumaila

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa jakadan kasar a Najeriya, Sali Almuzayen, ne ya sanar da shirin gwamnatin kasar na fara bayar da tallafin karatun a jihar Kaduna, lokacin da aka gudanar da taron ranar kasa na Kuwait karo na 64, wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Jakadan ya kuma bayyana cewa zasu bayar da ilimin firamare ga yara musamman mata da masu bukata ta musamman a jihar ta Kaduna.

Arewacin Najeriya dai na fama da matsalar rashin zuwan yara makatanta musamman firamare da sakandire.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here