Matatar fetur ta Dangote ta sake rage farashin litar man fetur zuwa Naira 825.
Hukumar gudanarwar matatar ce ta sanar da hakan a yau Laraba inda tace man zai yi sauki daga Naira 890, zuwa Naira 825, saboda a saukakawa yan Nijeriya a watan Azumin Ramadan.
Idan za’a iya tunawa a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara sai da matatar Dangote ta sanar da rage farashin man.