Shugaban Kasa Tinubu yace gwamnatin sa ta inganta hukumomin tsaron Najeriya don basu damar kakkabe tabarbarewar sha’anin tsaro yadda ya kamata.
Shugaban ya sanar da hakan a lokacin taron karawa juna sani na manyan jami’an yan sandan kasa karo na biyar daya gudana a Abeokuta dake jihar Ogun.
Yace gwamnatin sa ta fahimci alfanun dake cikin inganta harkokin tsaro wajen farfado da tattalin arzikin kasa, wanda hakan yasa aka samar da kayan aiki ga jami’an tsaro don daukar matakin gaggawa a duk lokacin da ake tsammanin samun rashin tsaro.
Shugaban kasar ya sanar da hakan ta bakin mataimakin sa Ƙashim Shettima, wanda ya wakilce shugaban a taron, inda ya nemi yan kasa su haÉ—a hannu da gwamnati tare da bawa jami’an tsaro gudunmuwar da suke bukata don cimma burin da ake dashi na kawo karshen rashin tsaro.