Hukumar JAMB ta sanar da lokacin rufe rijistar jarrabawar 2025

0
25

Hukumar shirya jarrabawar samun gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB, ta sanar da ranar 8 ga watan Maris 2025, a matsayin lokacin rufe yin rijistar jarrabawar shekarar 2025.

Hukumar tace bayan wannan wa’adin babu lallai a sake bayar da damar yin rijistar ga masu sha’awar zana jarrabawar JAMB.

Cikin wata sanarwa da hukumar JAMB ta fitar a yau Talata, ta jaddada cewa ba za’a kara lokacin yin rijistar ba, wadda aka fara a ranar 3 ga watan Fabrairu, kuma tun tuni an sanar da al’umma lokacin rufewar kafin yanzu.

Zuwa yanzu JAMB tace fiye da mutane miliyan 1 da rabi ne suka yi rijistar jarrabawar, kamar yadda kakakin hukumar Fabian Benjamin, ya sanar.

Sanarwar ta nemi duk mai shirin rubuta jarrabawar JAMB a shekarar 2025, ya gaggauta yin rijista kafin lokaci ya kure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here