Mahukuntan jami’ar Dutsin-ma Katsina (FUDMA) sun sanar da rufe jami’ar don yin hutun rabin zangon karatu, da zai fara aiki daga ranar 24 ga watan Fabrairu.
Rufewar ta biyo bayan zanga zangar da daliban makarantar suka yi bayan zargin jami’an tsaron sa kai na civilian JTF, da harbe dalibin jami’ar a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa an cigaba da yin zanga zangar daliban a safiyar yau Litinin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an JTF, ne suka harbe daya daga cikin daliban jami’ar bisa zargin cewa yana kaiwa yan ta’adda bayanan sirri.
Shugaban jami’ar FUDMA Farfesa Armaya’u Bichi, ne ya sanar da rufe jami’ar cikin wata sanarwa daya fitar bayan gabatar da taron majalisar zartarwa ta jami’ar.
Ya umarci dalibai su bar wajen kwanan su daga lokacin sanarwar zuwa karfe 6, na yammacin yau litinin.