Jam’iyyar NNPP bangaren Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, tayi watsi da dakatarwar da aka yiwa su Kawu Sumaila.
Shugaban tsagin jam’iyyar NNPP mai kayan marmari Sanata Mas’ud El-Jibrin ya jaddada cewa shi ne halastaccen shugaban Jam’iyyar, don haka basu dakatar da kowa ba.
Doguwa, yace Hashimu Dungurawa tsohon shugaban NNPP ne dan haka bashi da hurumin korar kowa daga jam’iyyar.