An saka ranar binne gawar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere

0
32

An bayyana ranar 3 ga watan Maris a matsayin lokacin binne gawar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Ayo Adebanjo, a mahaifiyar sa dake Ijebu Ode dake jihar Ogun.

Ayotunde Ayo-Adebanjo, da Adeola Azeez, da Obafemi Ayo-Adebanjo, ne suka bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka fitar a madadin iyalan mamacin.

 Sanarwar tace za’a fara bikin binnewar da wakoki bankwana ga Adebanjo a jihar Lagos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here