Rikicin cikin gida na neman mamaye APC a jihar Kano

0
126

Karamin ministan gidaje Yusuf Abdullahi Ata, yayi barazanar ficewa daga APC, in har aka sake kakaba musu Abdullahi Abbas, a matsayin shugaban jam’iyyar.

Ata ya yi wannan barazana a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, reshen Karamar Hukumar Fagge, jiya Asabar.

“Mun shaidawa kowa in har aka mayar da Abdullahi Abbas billahillazi duk irin mu fita za mu yi kuma sai jam’iyyar ta sake faduwa, inji Ata

Ya kara da cewa ko kadan baya tare da mutane irin su Abdullahi Abbas.

Ya ce irin kalaman da Abdullahi Abbas, ya yi na tuhumar Allah da izgili su ne su ka kayar da jam’iyyar APC a zaben 2023, kuma ya ce muddin aka sake baiwa Abdullahi Abbas shugabancin APC a Kano ba makawa sai jam’iyyar ta sake faduwa.

Karamin ministan yace an yi musu tarbiyya sun san waye Allah, sun san waye malami, sun kuma san waye babba, saboda haka ba za su sauka daga tarbiyyar su ba.

Yusuf Abdullahi Ata ya ce dole ne a chanza su Abdullahi Abbas a kawo mutanen kirki masu mutunci , saboda Allah ya sake baiwa APC mulkin jihar Kano, domin shi yake ba da mulki ba yawan kuri’a ba.

Ata, yace a zaben shekarar 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ne yaci zabe amma aka yi musu magudi, saboda izgilanci irin nasu Abdullahi Abbas, Allah ya hana APC nasara a kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here