Masu garkuwa da mutane sun sace tsohuwa a asibitin jihar Kano

0
218

Masu garkuwa da mutane sun kai wani hari a jihar Kano inda suka sace wata mata mai suna Talatu Ali mai shekaru 60 a asibitin masu fama da taɓin hankali na dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

Tsohuwar da aka sace ta kasance mai jiran kulawar likitoci a asibitin mahautan kafin wannan mummunan lamarin ya faru da ita.

Mai bayar da rahoton sha’anin tsaro Zagazola Makama, yace ɗan matar da yar uwarta ne suka kaita asibitin daga kauyen yar gaya na karamar hukumar Dawakin Kudu, a ranar 19 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:30, na safiya don ganin likita.

Yan uwan matar sun neme ta sun rasa a lokacin da take kan layin ganin likita.

Iyalan nata sun yi duk mai yiwuwa amma basu ganta ba, wanda hakan yasa suka kai rahoto ofishin yan sanda na Dawanau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here