Babangida ya sanar da dalilin sa na kifar da Gwamnatin Buhari

0
56

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ce sun hambarar da gwamnatin Muhammadu Buhari ne saboda bai amince da manufofin salon shugabancin Najeriya ba na wancan lokaci.

Babangida dai shi ne shugaban ma’aikata na Buhari lokacin da yake shugaban kasa na soji.

IBB, ya sanar da hakan a cikin rayuwar sa daya wallafa, kuma aka kaddamar da shi a Abuja ranar Alhamis.

Buhari shine ya hambarar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari a juyin mulkin ranar 31 ga Disamba, 1983.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here