Jami’an yan sanda sun harbi wani ma’aikacin hukumar kula da shige da fice ta kasa (immigration) Christian Oladimeji, lokacin da wasu bata gari suka farmaki yan sandan yayin da ake kokarin kwato wasu kayan da bata garin suka sace a jihar Neja.
Mai wallafa rahoto akan sha’anin tsaro Zagazola Makama, yace lamarin ya faru a jiya juma’a da misalin karfe 12:30, na rana.
Makama yace yan sanda da suka harbi jami’in lokacin da suka taho domin kwato wasu karafan da aka sato, wanda ake yin aikin kwangila dasu.
Lamarin ya haddasa lalacewar motar sintirin yan sandan lokacin da bata gari suka rika jifan yan sandan da duwatsu.