Rundunar Hisbah ta jinjinawa yan uwan Y Amerika Dan TikTok

0
33

Rundunar Hisbah ta jihar Kano, ta yabawa yan uwan fitaccen dan TikTok Y Amerika, wanda yake yada badala a shafin sa na TikTok.

Yan uwan jarumin TikTok din sun hadu a gida tare da daukar matakan ladabtawa akan dan uwan nasu ta hanyar zane masa jiki har sai da ya furta cewa ya dena aikata mummunan laifin yada badala a shafin sa na TikTok.

A lokacin da suka dauki matakin Y America, ya sanar da cewa ya dauki nasihar da aka yi masa kuma ya tuba.

Haka ne yasa rundunar Hisbah ta jihar Kano ta yabawa yan uwan nasa bisa namijin kokarin da suka yi na yiwa dan uwan su tarbiyya.

Rundunar Hisbah ta yabawa yan uwan Y America ta hannun babban daraktan ta Abba Sa’idu Sufi, inda suka je har jihar Kaduna don zantawa da ahalin Y America.

Babban daraktan, yace tabbas ya kamata a jinjinawa yan uwan Y America, saboda sun yi abun daya dace, inda yace kamata yayi kowa ya rika gyara barakar da ya gani tun daga gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here